Sojoji Sun Bude Wuta Kan ‘Yan Shi’a Masu Tattaki Zuwa Abuja

0 118

DA DUMIDUMINSA

Sojoji Sun Bude Wuta Kan ‘Yan Shi’a Masu Tattaki Zuwa Abuja

Daga Bilya Hamza Dass

Rahotanni daga garin Suleja dake kan hanyar Kaduna sun tabbatar da cewa an samu wata mummunan a rangama tsakanin rundanar Sojojin Nijeriya da tawagar ‘yan Shi’a masu tattaki daga kafa zuwa garin Abuja a daidai gadar Zuba kilomita kadan kafin shiga garin na Abuja.

Wani ganau mazaunin wajan da abin ya faru ya tabbatar min da cewa kimanin awa guda kafin faruwar abin an ga manyan motocin sojoji suna shawagi a wajen.

Rahotanni sun nuna akalla mutane 10 ne suka rasa rayukan su, sama da dari sun samu munanan rauni.

Leave A Reply

Your email address will not be published.