Sojoji sun kama dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo

0 185

Sojojin sun kama wani kwamandan kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.

Babagana Abubakar wanda akafi sani da suna Alagarno ya shiga hannun sojojin rundunar sojan Najeriya a unguwar Bulabulin Ngarnam dake wajen birnin Maidugurin jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Sani Usman Kukasheka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ya bayyana cewa an kama Abubakar ne a wani gida da yake boye a unguwar.

Usman ya ce an kama Alagarno da wasu kayayyaki da suka hada da hular kwano ta sojoji guda biyu, takalmin sojoji, jakar goyo ta sojoji,katin zabe da kuma sauran kayayyaki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.