Sumayyar Zamfara – Yadda cikina ya zube a hannun masu garkuwa da mutane

0 195

Sumayya Abubakar Dauran mai juna biyun nan da masu garkuwa da mutane suka sace tare da ’yan tagwaye a Jihar Zamfara ta samu kubuta, bayan ta kwashe makonni goma a tsare.

Lokacin da Aminiya ta gana da ita, ta bayyana kuncin rayuwar da ta yi a cikin daji tare da masu garkuwa da mutanen, inda ta ce wadanda aka sace su tare da farko suna da yawa, mata 12 yara kanana 4, manyan maza 7. A hankali suka tafi, aka bar ta ita kadai  tare da su.

“Na yi rayuwar kunci da takaici a hannun masu garkuwa da mutanen da suka sace ni. Kwana 70, wato mako 10 na yi hannunsu ban yi wanka ba. Har na dawo gida ban canja kayan da nake sanye da su ba, don ko sun kai mu tafki nakan ki yin wanka, domin ba na iya yin tsiraici a gaban jama’a.

“Wata rana suna ba ni omo ko sabulu in wanke zanena da hijabi. Ina dafa musu abinci su ci mu kuma sukan ba mu shinkafa ita kadai mu ci, ba na koshi amma ba na yin barcin kirki. Akwai lokacin da na yi mako uku cur ni kadai ce mace a wurin. Yadda na ga safiya haka nake ganin dare, barci ba ya dauka ta; rabi da rabi nake yin sa,” inji ta.

Sumayya ta ci gaba da cewa: “Kai ne za ka dafa abincin da za ka ci. Lokacin da su Hassana na nan, muna cin shinkafar cikin roba. Bayan sun tafi ne masu garkuwar suka zo da matansu cikin dajin, sai aka mayar da robobin hannunsu gaba daya, muka koma cin abinci a leda kamar wasu karnuka.”

Da wakilinmu ya tambaye ko an yi mata fyade a lokacin zamanata a can, sai ta ce: “Masu garkuwar manya ne suke kamo mutane, matasa kuma ke tsaro a daji. Lokacin da suka kamo mu sun gaya mana cewa duk wadda wani daga cikin matasan ya so ya yi mata wulakanci ko ya nemi yi mata fyade, mu fada musu. Suka ce idan ba mu fadi ba mun cuci kanmu da su. Idan kuma suka samu labarin an yi mana muka boye, to za su kashe mu.”

“A cikin masu tsaron namu akwai wanda ya so ya keta mutuncina amma da na rika kuka, sai ya ce tunda ba na so shi ke nan. Marigayi Sirajo (wanda aka kama mu tare) ne ya ba ni hakuri, ya ce tunda bai taba ni ba, kada mu fada wa manyan, domin daga baya yaran na iya yi mana illa in manyan ba su nan. A haka na dauki alkawarin cewa duk wanda ya yi fasikanci da ni da karfi ya samu galaba kaina, na ce sai na gaya wa manyansu. Alwashi ne na dauka,” inji ta.

“Akwai wata rana ina kwance sai wani cikinsu ya zo ya rika dukana wai sai in tashi. Ni kuwa na ce ban tashi. Ya ce in ban tashi ba zai kashe ni, na ce sai dai ya kashe ni. A wannan bugun da ya yi mini sai da yatsata ta yi jini. Allah ne Ya tsare ni. Kuma akwai wata matar aure da aka kamo da dare sai da daya daga cikinsu ya keta mata haddi, ya gargade ni cewa idan na fada wa manyansu sai ya kashe ni. Ya ce zai bari in zai raka ni zuwa fitsari ya harbe ni, ya ce guduwa zan yi. Amma na fada mata cewa manyansu ba su bari a rika yi wa mata wulakanci, in ta san yadda za ta yi ta rika kare kanta ta yi, in kuwa ta kyale za su sanya mata ciwon da har ta mutu ba ta rabuwa da shi,” inji Sumayya.

Batun juna biyun da take dauke da shi kuwa ta ce ya samu matsala. “Akwai wata tafiyar da muka yi saman babur tun cikin dare muke tafiya cikin dokar daji har kusan gari ya waye. Kafin mu isa inda suke so a tafiyar ne muka fadi a babur din, na ji wani abu ya taso min tun daga kafafuna har cikin idona. Akalla na yi awa biyu ban san inda nake ba. Bayan na dawo hayyacina ne na ga ashe cikina ne ya zube,” inji ta.

“A gabana suka kashe Sirajo, sun kashe shi ne saboda wata rana ne dayansu yana magana da wanda ake ciniki da shi kanmu suke fada masa cewa ba ’yan tagwaye suka tafi dauka ba, ni ce suke son dauka. Amma sun karbi Naira miliyan 15 gare su, ni da suka tafi kamu ba za su sake ni ba sai an ba su Naira miliyan 20. Wanda yake magana da su ya ce ba su da kudin amma suna da Naira miliyan biyar, suka ce lallai sai Naira miliyan 20. Suka ce Sirajo kuwa tunda babana zai karbe shi, to Naira miliyan 10 zai bayar ko yanzu su harbe shi. Ana haka wayar ta tsinke, sun dauka kila wulakanci ne aka yi musu. Washegari suka ce mana ko ni ko Sirajo yau sai sun kashe daya. A nan take suka kira wanda suke magana da shi ya kawo masu Naira miliyan 20 nawa, ya ce to Allah Ya sauwaka. Hakan da ya ce ya ba su haushi, kare wayar ke da wuya suka gaya wa Sirajo ka yi hakuri, kashe ka za mu yi. Bai ce komai ba suka goya mu saman babur, da aka kai kusa da wani rami suka jefa shi suka harbe,”  ta fadin haka tana kuka.

Sumayya ta fadi yadda mutanen ke harkokinsu a dajin: “Mutane suna zuwa daban-daban, in ka ga wannan fuskar yau, gobe wata za ka gani amma dai Hausawa da Fulani ne. A kiyasi za su kai 100, sai ka ji suna fadin cewa sun kai 400 a dajin, akwai matansu cikin dajin, duk da muna mata amma ba su taba tausaya mana ba har hantararmu da zagi suke yi, su ce mu bar kallonsu kada wata rana mu hadu da su a gari mu tona musu asiri.  Su da mazan nasu ba su rufe fuskokinsu gare mu. Duk namijin da suka kamo suna daure shi da sarka. In sojoji suka kawo farmaki suna daukar matansu a babur su kai karkara su boye. Sun yi artabu da sojoji ya kai sau biyar ina wurin. In kura ta lafa sukan nuna mana su suka yi nasara,” inji ta.

Ta ce “Wurin da suka aje mu sun ce daba hudu ce amma daba biyu ce wuri daya tare suke tafiya yin komai. Mutum hudu suke bari a daji don tsaron wadanda aka kamo, biyu daga cikin matsaran ne ke kokarin lalata da mata. Daya daga cikinsu yana da mata, yakan tafi ya yi kwana uku ya dawo. Kafin in baro wurin sun kamo wadansu mutum 20 ’yan Karamar Hukumar Illela ta Jihar Sakkwato. A fadan da suke da sojoji ne ya sanya suka karbi kudin fansata Naira miliyan 10, in ka hada da na farko Naira miliyan biyar. Da suka ki aminta suka rike tsohon mutane sun zaci babana ne, don sun fada mini cewa sai sun hada ni da babana wuri daya a dajin. Naira miliyan 15 aka fanso ni.”

Ta ce yadda suke rabon kudin fansar shi ne masu tsaronsu a daji in an biya kudi ana ba su Naira dubu 50 zuwa 100. Kudin su Hussaina da aka karbo, an bai wa masu tsaron Naira dubu 100, manyan kusan sun samu Naira dubu 700 kowannensu bayan an fitar wa mai gidansu kudin bindiga, kamar yadda ta ce ta ji suna labari.

Mahaifin Sumayya Alhaji Abubakar Dauran ya ce Naira miliyan 15 suka biya aka saki ’yarsa da Alhaji Lauwali ’Yandoto da aka rike a lokacin da ya kai Naira miliyan 5 don a saki Sumayya a farko. Daga bayan nan suka hada Naira miliyan 10 aka kai musu, domin sun ce in aka wuce karfe uku na Litinin ba a kawo kudin ba, za su kashe su. A haka suka samu rance aka je dajin Rukudawa aka kai musu kudin, aka dawo da Sumayya da Alhaji Lauwali amma Sirajo sun kashe shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.