Teema Makamashi Tace Shaye-shaye ko neman kananan yara za’ayi da kudin da Ummi Zeezee tace abokan aikinta sun cinye

0 1,191

Bayan da taurruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta caccaki wasu daga cikin abokan aikinta akan cinye kudin da ta yi zargin sun yi wanda tace dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya bayar a rabawa ‘yan Kannywood, abokiyar aikinta, Teema Makamashi ta mayar da martani me ban mamaki.

Teema ta baiwa Ummi amsar cewa, Wallahi ba abinda zai musu karshema shanye kudin za ayi a shaye shaye ko kuma anemi yara kanana da kudin azzalumai kawai.

Wannan dai ya jawo wasu na tambayar cewa kada kudi yasa su rika tonawa abokan sana’arsu asiri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.