VIDEO: Gasar Rawa Tsakanin Ado Gwanja Da Amaryar Sa Abun Birgewa

0 357

Yan uwa da abokan arziki ciki har da abokan sana’ar shi daga masana’antar Kannywood sun halarcin bikin kamu da aka gudanar daren ranar Alhamis.

Shahararren mawaki kuma jarumi, Ado Isah Gwanja, ya shiga cikin yanayin biki don raya sunnan fiyeyyen halitta.

An gudanar da bikin Kamu na daga cikin shagulgulan bikin auren sa da amarya Maimuna Kabisr Hassan.

Bikin Kamun ya samu halartar yan uwa da abokin arziki ciki har da abokan sana’ar shi na masana’antar nishadi.

Cikin fitattun jarumai da suka halarci bikin kamun wanda aka gudanar daren ranar Alhamis 11 ga watan Oktoba akwai Adam A.Zango da Maryam Yahaya da Ahmad Shanawa.

Tuni dai fitaccen mawakin wanda ake ma lakabi da “Limamin Mata” yake nuna farin cikin sa bisa dacewar da ya samu haduwa da sahibar sa.

Ga masu bibiyan shafukan sa na kafafen sada zumunta, za’a tabbatar da cewa yana yawan bayyana farin cikin sa bisa kaunar da yake ma amaryar sa tare da wallafa hotunan su.

Leave A Reply

Your email address will not be published.