Wani Miji Ya Saki Matarshi Shi Sabida Ta Zabi Buhari

0 320

Wani magidanci mai suna Abdullahi Yadau ya saki mai dakinsa bayan sun samu rashin jituwa dangane da bambancin ra’ayin siyasa a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya.

Abdullahi ya shaida wa BBC cewa ya yi wa matarsa Hafsat Suleiman saki biyu ne bayan da ta sha alwashin cewa “ita Shugaba Muhammadu Buhari za ta zaba a zaben 2019.”
Ya ce har sai da maganar ta kai gaban iyayenta, inda daga nan ne sai ya yanke hukuncin sakinta wanda kuma “har ya balla mata hakori,” a cewarsa.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin mai dakinsa Hafsat, sai dai hakan ya ci tura.

Saurari hirar da BBC ta yi da Abdullahi Yadau

Abin da ba ku sani ba game da AtikuBuhari da Atiku sun raba kan malaman IzalaBuhari ya ce ya dace likita ya duba ObasanjoAmma mun yi magana da yayanta mai suna Ibrahim Suleiman, wanda ya bayyana bacin ransa game da abin da ya faru. Kuma ya sha alwashin cewa “ba za ta koma dakinta ba.”
Da alama zaben 2019 zai fi wadanda suka gabace shi ta fuskar rabuwar kawunan al’umma da ke mara wa mabambantan ‘yan takara baya.
Wasu masu sharhi kan al’amura a kasar suna ganin hakan bai rasa nasaba da yadda duka manyan ‘yan takarar biyu suka fito daga yanki guda – wato arewacin kasar kuma dukkannsu Musulmi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.