Wani Shugaban ‘Yan Sanda Ya Tonawa Tsohon Shugaban kasa Goodluck Asiri

Wani Dan Sanda Ya Fallasa abin da ya faru lokacin rikicin Tambuwal da Jonathan

0 438
Wani Dan Sanda Ya Fallasa abin da ya faru lokacin rikicin Tambuwal da Jonathan

-Tsohon Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Sulaiman Abba ya kara yin fashin baki game da wasu abubuwa da su ka faru daf da zaben 2015 lokacin Goodluck Jonathan yana mulki.

Sulaiman Abba wanda yanzu ya ajiye aiki ya shiga siyasa yayi hira da Jaridar Daily Sun inda ya karyata wasu zargin da ake yi masa na yaudarar Shugaba Jonathan ko kuma hada-kai da Janar Muhammadu Buhari bayan ya lashe zaben 2015.

Tsohon Sufetan na ‘Yan Sanda ya kuma bayyana cewa Dr. Jonathan ne ya bada umarni a janyewa tsohon Kakakin Majalisa Aminu Tambuwal Jami’an tsaro. Abba yace yayi kokarin yi wa Jonathan bayani akasin haka amma sam bai fahimta ba.

A wancan lokaci dai an tube Rt. Hon. Aminu Tambuwal bayan sauya-shekar da yayi daga PDP zuwa Jam’iyyar APC mai adawa. Sulaiman Abba yace shugaba Jonathan a wancan lokaci ya nemi har DSS su janye masu gadin Hon. Tambuwal a Majalisa.

Tsohon Shugaban na ‘Yan Sandan Kasar ya kuma bayyana cewa sun samu labari cewa Jonathan ya sha kashi a zaben na 2015 tun kafin labarin ya iso fadar Shugaban kasa. Abba yace yayi kokarin hana Mabiya Jonathan su tada rikici a wannan lokaci.

A hirar har wa yau, Sulaiman Abba yayi magana game da zargin da jama’a ke yi wa tsohon Shugaban kasa Jonathan na shan giya. Abba mai ritaya yace bai taba ganin Jonathan yana shan giya ba kuma mutumin kirki ne fiye da tunanin Jama’a.

Leave A Reply

Your email address will not be published.