Wani Uba ya kashe ‘yar sa da Duka donta dame shi da kuka – a Kano

0 154

‘Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta kama wani Uba da ake zargi da kashe ‘yarsa ‘yar shekara uku a jihar Kano saboda ta dame shi da kuka.Mahaifin mai suna Sani Lawal da ke Unguwar Kofar Gabas a karamar hukumar Rimin Gado, yana hannun ‘yan sandan jihar Kano yanzu haka, inda ake ci gaba da gudanar da bincike.Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Magaji Musa Majiya wanda ya tabbatar wa da BBC da faruwar al’amarin, ya ce mutumin da ake zargi ya yi amfani ne da maganin kashe kwari da ake kira Fiyafiya domin halaka yarinyar don ya huta da kukan da ta dame shi saboda raunin da ta ji a kafartaYarinyar ta rasu ne bayan an garzaya da ita asibiti, kamar yadda kakakin ‘yan sandan ya shaida wa BBC.Musa Majiya ya ce mahaifin yarinyar sun rabu da mahaifiyarta, kuma yarinyar tana hannun kakarta da ke rikonta, kuma an kawo ta ne don ta ga mahaifin da ke gadin turken sadarwa na salula.’Yan sandan sun ce za su gabatar da shi kotu domin fuskantar shari’a.

Leave A Reply

Your email address will not be published.