Wata Budurwa Zata Shade Shekaru Biyu (2) a Gidan Yari, Sabida Ta Rumgume Wani Mawaki a wani Gidan wasa

0 369

Wata Budurwa Zata Shade Shekaru Biyu (2) a Gidan Yari, Sabida Ta Rumgume Wani Mawaki.

An kama wata budurwa a kasar Saudiyya saboda ta rungumi wani mawaki daya birge ta a gidan wani wasa dake birnin Ta’if, kamar yadda ‘yan sandan kasar suka sanar a ranar Asabar.

Budurwar ta fita daga cikin mutanen da suka halarci kallon wasan gabatar da wakoki da mawakin kasar Saudiyya, Majid Al Mohandes, tare da hawa kan munbarin da yake inda ta rungume shi cikin shauki da birgewa.

Take aka kama budurwar kuma aka damka ta hannun wata hukuma dake kula da tsare mata da suka aikata laifi kafin a tura su kotu, kamar yadda kakakin hukumar ‘yan sanda a kasar ta Saudi ya sanar das ashen yada labarai na Sabq.

Wata budurwa a kasar Saudiyya zata shafe shekaru 2 gidan yari saboda rungumar mawaki a gidan rawa

Kakakin ya sanar da Sabq cewar, budurwar ta aikata laifi bisa dogaro da wata doka da kasar tayi a watan Mayu.

Laifin da budrwar ta aikata na da hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari da kuma tarar Riyal 100,000 kamar yadda jaridar kasar Saudi, Okaz, ta tabbatar. Ba a ambaci sunan budurwar ko adadin shekarunta na haihuwa ba.


A wani faifan bidiyo dake yawo a dandalin sada zumunta, an ga budurwar, sanye da doguwar abaya da ta rufe fuskarta zuwa kafafu, ta hau kan munbarin da mawakin yak e cikin shauki tare da rungume shi.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.