Wata Sabuwa: An Sace Amarya Kafin Aure

0 398

An bayyana satar wata amarya mai suna Olanike wadda aka sake ana kwana daya kafin bikin ta. Ance dai tayi kwana 6 a hannun barayin.

An ruwaito cewa an sace amaryar ne a gaban gidan su dake a jihar Ondo tare da danta kafin daga baya a gano su bayan sun shafe sati 1 a hannun barayin. Dole nema hakan yasa aka dage bikin. Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa barayin sun hada kai ne da wasu daga cikin yan uwan ma’auratan.

Wani daga cikin barayin mai suna Ayodeji wanda kuma nakasasshe da matar sa ne ake zargi da laifin taimaka musu. Jaridar ta cigaba da cewa lokacin da aka saidawa angon lamarin sai yayi sauri yaje ya shaidawa yan sanda dake garin.

Barayin dai daga baya sai suka yada yaron da kuma motar don kada agano su amma bayan kwana 6 sai gashi angano su tare da wadda suka sace din. Philip Ezekiel wanda dayane daga cikin barayin ya amince da zargin da akayi masa inda kuma ya shaida cewa Ufoma Godwin ne shugaban su. Godwin din dai yanzu haka yana asibiti sakamakon ciwuka da ya samu na harbin bingida. Hilda Harrison wadda itace kwamishinar yansanda ta Ogun tace za’a gurffanar da su gaban kotu idan an gama binciken da akeyi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.