Wata Sabuwa: Shugaba Buhari Zai Mika Mulkin Nijeriya A Shekarar 2023 -Inji Osinbajo

0 242

A jiya Asabar, 22 a watan Dasumba, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa, mulkin kasar nan a shekarar 2023, zai kasance a hannun yankin Kudu maso Yammacin Najeriya muddin suka marawa shugaba Buhari baya a zaben kasa na badi.

Osinbajo ya jaddada cewa, Yarbawa ke da cancantar jagorancin kasar nan a 2023 da kuma hakan ba zai tabbata ba face shugaban kasa Buhari ya yi nasara a zaben 2019. Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tawagar Mataimakin shugaban kasa ta hadar da gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo, dan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar APC a jihar; Cif Bayo Adelabu da kuma saura jigan-jigan jam’iyyar APC na jihar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.