Kalli Wata ‘yar Saudiyya ta ce ‘yan uwanta za su kasheta saboda ta yi ridda

0 129

Wata mata ‘yar Saudiyya ta shiga wani mawuyacin hali a babban filin jirgin sama na Bangkok bayan da ta tsere daga gida kuma wani jami’in Saudiyya ya kwace mata fasfonta.

Rahaf Mohammed al Qunun ta ce da farko tana kan hanyarta ta zuwa kasar Kuwait ne, sai ta shiga wani jirgin domin tsere wa ‘yan uwan nata kwanaki biyu da suka gabata.

Tana kokarin ta isa kasar Ostreliya ne ta hanyar shiga wani jirgin da zai kai ta can daga Bangkok.

Ta fada wa BBC cewa ta fita daga Musulunci, kuma tana tsoron za a tilasta mata komawa Saudiyya, inda ‘yan uwanta za su iya kashe ta.

Wakilin BBC a Bangkok Jonathan Head ya ce Rahaf al-Qunun a firgice take matuka. Ta ce tana da bizar Ostreliya amma wani jami’in diflomasiyya na Saudiyya ya kwace fasfonta a lokacin da ta sauka daga jirgin sama a filin jirgi na Suvarnabhumi.

Shugaban ‘yan sandan Thailand Manjo Janar Surachate Hakparn ya sanar da BBC cewa matar ta tsere wa auren dole ne.

Ya ce saboda ba ta da izinin shiga kasar Thailand, shi yasa suke kokarin mayar da ita inda ta fito ta jirgin da ya kai ta can wato Kuwait Airlines.

Janar Surachate ya ce bai san komai game da batun kwace mata fasfo ba.

Amma ‘yan Saudiyya na iya neman biza bayan sun sauka a kasar, wato ba sai da biza za su iya zuwa Thailand ba.

Matar ta bayyana halin da take ciki a shafinta na Tiwita, tana cewa: “Saboda bani da yadda zan yi, bari in bayyana ainihin sunana da dukkan bayanai na.”

Ta kuma nuna hoton fasfonta “domin ina son a san cewa ba da gaske nake”.

A wani sakon kuma ta wallafa cewa: “Ina tsoron ‘yan gidanmu za su kashe ni”.

Wannnan lamarin yayi kama da na wata ‘yar Saudiyya da ita ma ta sami matsala a kan hanyarta ta zuwa Ostreliya a 2017.

Ita ce Dina Ali Lasloom mai shekara 24 wadda ke kan hanyarta ta zuwa kasar Filifins daga Kuwait, inda ‘yan uwanta suka tilasta mata komawa Saudiyya daga filin jirgi na Manila.

Ta yi amfani da wayar salular wani matafiyi dan kasar Kanada wajen aikawa da sakon bidiyo da aka wallafa a Tiwita da ke cewa ‘yan uwanta za su kashe ta.

Har yanzu babu wanda ya san halin da ta ke ciki bayan da aka mayar da ita Saudiyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.