Ya Kamata Ko Wane Dan Nijeriya Ya mallaki Bindiga, Domin kare kanshi, Inji Sanata Kabiru Marafa.

0 157

Ya Kamata Ko Wane Dan Nijeriya Ya mallaki Bindiga, Domin kare kanshi, Inji Sanata Kabiru Marafa.


“Manufa ta a nan ita ce, bai yiwuwa kowace rana a rika bi gida-gida ana yi wa mutane yankan-rago.

” Mai yiwuwa kowanen mu na neman a sahale masa mallakar bindiga. A bar kowa ya mallaki bindiga, domin idan ma ka tunkari gida na dauke da bindiga, ko ka sani fa ni ma ina da tawa bindigar.”

Furucin Sanata Kabiru Marafa ke nan, wanda ke wakiltar Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, wanda da ji kowa ya san ya yi matukar fusata da irin yawan kashe-kashen da ake yi a kasar nan da kuma yadda al’umma ke mutuwar kiyashi ba tare da iya kare kan su ba.

Jihar sa Zamfara na ta fama da hare-haren ‘yan ta’adda masu kashe daruruwan jama’a, musamman a cikin 2018 din nan da abin ya fi kamari.

Baya ga kashe-kashe, ana kone dukiyoyin jama’a da banka wa gidajen su wuta tare da satar dabbobin su.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai ya yi wancan furuci na sama, a zauren Majalisar Dattawa.

Marafa ya ce ya yi imani abin da kawai dan ta’adda ya zarce sauran mutane, shi ne bindiga ko makamin da ya ke dauke.

Sai ya ce duk wanda ya san kai ma ka na da makami irin na sa ko wanda ma ya fi nasa, to zai yi shakkar tunkarar ka.

Marafa ya sha mikewa a zauren majalisa ya na magana a kan a magance kashe-kashe a kasar nan, musamman a jihar Zamfara.

Ya kuma sha sukar Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari ya na cewa ya maida kashe-kashen siyisa, shi ya sa bai damu da gaggauta magancewa ba.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.