Yadda Ake Gyara Jiki A Gargajiyance (Muhibbat)

0 340

Yadda Ake Gyara Jiki A Gargajiyance (Muhibbat)


Masu karin magana sukan ce, ‘ba a tauna taura biyu a lokaci guda’, ko kuma a ce ba a saka karfe biyu a wuta da nufin tada komadar kowanne kuma a lokaci guda. Sai dai za mu iya cewa a wannan zamanin ga dukkan alamu akwai wadanda suke da basira ta tauna taura biyu a lokaci daya. Bakuwarmu ta Adon Gari a wannan makon kwararriya ce wajen gyaran jiki ta ingantacciyar hanyar amfani da kayan gargajiya. Sannan jaruma ce da ta hada manyan ayyuka da take yi a rayuwarta. Baya ga kasancewarta matar aure wadda take hidimar kula da iyali, har ila yau darakta ce, furodusa (mai shirya) fim ce sannan ga wasu ayyuka na daban da ta hada da suka shafi harkokin kasuwanci. Domin jin yadda take aiwatar da wadannan ayyuka da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarta, a karanta tattaunawar da muka yi da ita tun daga farko har zuwa karshe:
Za mu so ki fada mana Sunanki da cikaken tarihin rayuwarki?
Sunana Muhibbat Abdulsalam, Mrs Giggs. An haife ni a garin Kaduna, kuma na yi karatuna a Kaduna na boko da na Addini.
Wace shekara kika fara fim kuma Me ya jawo ra’ayinki kika shiga harkar?
Na fara fim a karshen 2000 da fim din Imani. Da farko dai sha’awar sana’ar fim ne ya shigo da ni, asali ma fim din Sangaya ne ya shiga raina sosai.
A matsayinki ta matar aure kuma jaruma kuma daracta kuma ’yar kasuwa, yaya kike iya tafiyar da harkarki da kuma kula da iyalinki?
Gaskiya, ba abu ne mai sauki ba amma dai ina bakin kokarina. Kusan in ce, sana’o’ina da dan yawa, Ina rubuta labari, Ina sarrafawa, Ina yin kwalliya ta amare, muna abincin biki, muna gyara jikin amare da sauransu, kawai ni ban yarda da zaman banza ba, kuma mafi yawancin ayyuka na a gida nake yin su, sai dai idan zanyi tafiya ne, amma ina da mai kulan min da yara. Alhamdu lillah muji na taimaka min ta ~angaren kasuwancina da kuma kula da yara idan bana nan.
Wane ci gaba kike ganin an samu yanzu a harkan fim?
An samu cigaba ta bangaren kayan aiki sosai.Wanw kira za ki yi ga mata masu son su shiga harkar, kuma yaya kike ganin makomar rayuwar mace a harkar.Shawarar ita ce ba a harkar fim kadai ba, a kowace irin sana’a ce, yana da kyau mace ta rike mutuncinta, dan kuwa ba ki san waye mujinki ba, ba ki san a ina mujinki yake ba. Makomar mace a harkar fim kuwa kamar yadda na fada ne, idan kika rike mutuncin kanki, inshaa Allah makomarki za ta zama mai kyau. Kuma kar mace ta tsaya a fim kadai, ta hada da karatu da kuma koyon sana’ar hannu.
Bari mu dan koma amsarki ta sama. Ko za ki fada mana yadda kike yin gyran jiki da abincin biki da kika ce?
Gyara jiki ina yin sa ne da kayan gargajiya, kamar su kurkur, dilka, garin alkama, madara, lemon tsami da sauransu.
Idan aiki ya same ki a wani gari daban ta yaya kike raba kanki, a matsayinki na mai sarrafawa kuma da ba da umurni. Za ki iya barin ’ya’yanki mata su fito a fim?
Ya danganta, gaskiya aikin da ya fi romo shi nake yi. A da idan na samu aikin gyaran jiki a wani gari ina zuwa, amma yanzu ba na zuwa, sai dai mutum ya sayi kayan gyaran jikin a wurina sai in yi masa bayanin yadda zai yi amfani da shi. Idan suna son yin zan bar su, amma gaskiya ina so su yi karatu sosai kamar yadda na samu ilimi. Kuma ni na dauki fim sana’a babba.
Yanzu Misali mace tana son shiga harkan fim ta hanunki ya za ta yi ta same ki?
Ayya! Ni ba a shiga fim ta hanyata. Za ta je dai ta yi rajista da kungiyar ‘yan fim, idan sun tantance kuma sun ba ta kati sheda, shi ke nan, to idan har akwai irin rawar da za ta taka a tsarin labarina sai a saka ta.
Ko akwai wani sako da kike son fada da ba mu tambaye ki ba?
Sakon shi ne, dan Allah masoya a dinga taimaka mana da addu’a, a daina jifar mu da munanan kalmomi.Mun gode kwarai da hadin kan da kika ba mu.Ni ma na gode, shukuran jazeela.

Sources:leadershipayau.com

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.