Yadda Auren Amarya Ya Kusa Mutuwa Saboda Amfani Da A Cuci Maza (2)

0 1,035

Ana cikin haka ne sai Ramlat ta hadu da Faruk. Faruk ya fito ne daga gidan masu kudi. Ba a  kasar nan ya yi karatu ba, kuma saurayi ne mai son macen da ta hadu, kuma take ji da kanta.  A takaice yana son mace mai  kyale-kyale kamar Ramlat.

Ya hadu da Ramlat ce a lokacin da ta je kasuwa yin cefane. A kan hanyarta ta komawa gida ne ya hange ta yana cikin hadaddiyar motarsa, inda nan take bai yi wata-wata ba ya taka birki, kuma ya yi mata sallama, ita kuma ta amsa ciki-ciki don jan aji, kamar yadda wadansu ’yan matan yanzu ke yi wa samari.

Bayan sun gaisa ne sai ya tambayi unguwar da take, inda ta yi masa kwatance, kuma suka yi musayar lambar waya.

Abinka da mai kwadayi, tuni ta tsunduma cikin soyayya da Faruk musamman ganin yadda ya hadu kuma yana hawa irin motar da take so.

Bayan kwana biyu suna hira a waya sai Faruk ya kai mata ziyara gidan da ta yi masa kwatance.  Ashe Ramlat ba ainihin gidan da take ta yi masa kwatancen ba. A duk lokacin da ta fahimci zai je wajenta sai ta shiga wani kasaitaccen gidan wata kawarta a  makwabta mai suna Shamsiyya. Idan Faruk ya isa kofar gidan sai ya kira ta a waya sannan ta fito.  Da zarar sun gama hira sai ta tabbatar ya bace sai nan ta nufi kofar gidansu na ainihi, gidan talakawa.  Ramlat tana yin haka ne don ta nuna wa Faruk lallai tana da aji, ita ba talaka ba ce.

Kawarta Shamsiyya ta sha yi mata nasiha a kan ta daina irin wannan hali, ta fito fili ta fada wa Faruk gaskiya, idan yana son ta zai aure ta, in kuma ba ya son ta, sai ya rabu da ita. Ita kuma ta nemi wani, amma ta ki jin wannan shawara.

Sun dade suna tafiya a haka, sai ran nan Faruk ya yanke shawarar zai aure ta.  Hasali ma ya fada mata tuni ya sanar da iyayensa, don haka ya kamata ta gabatar da shi wajen iyayenta don a tsayar da magana.

Jin haka sai hankalin Ramlat ya tashi, ta nemi kawarta ta sanya iyayenta don su zame mata waliyyai, tunda mahaifinta ya rasu, kuma ba ta da wani na gaba da zai tsaya mata a kan batun aurenta in ban da mahaifiyarta.

Iyayen kawarta Shamsiyya suka amince, kuma suka yi maraba da zama waliyyan Ramlat game da batun aurenta.

Ba a dade ba aka sanya ranar biki. Bayan an yi shagali ne sai Faruk ya tare da Ramlat a wani gida na musamman da mahaifinsa ya gina musu.

Za mu ci gaba insha Allah

Leave A Reply

Your email address will not be published.