Yadda Auren Wata Amarya Ya Kusa Mutuwa Saboda Amfani Da A Cuci-Maza

0 447

Akwai wani saurayi  mai suna Faruk (ba sunansa na gaskiya ba) da yake neman wata yarinya da aure mai suna Ramlat (ita ma ba sunanta na gaskiya ba).  Suna gari daya ne amma ba unguwarsu daya ba.

Ramlat ba ta wuce shekara 19 ba, budurwa ce mai takama da ji da kai.  Hasali ma ma yarinya ce da ba kowane namiji take kulawa a rayuwarta ba. Hakan ya sa samari da yawa suke  shakkar yi mata magana ko  hulda da ita.

Duk da Ramlat ta fito ne daga gidan talakawa, amma takan dauki kanta tamkar wadda ta fito daga gidan masu kudi. Dalili shi ne saboda yanayin shigarta da yadda take ji da kanta musamman idan ta shiga cikin jama’a ko tana tafiya a kan hanya. Yadda take tafiyar kasaita d ji-ji-da-kai, na ba mutane mamaki musamman wadanda suka san asalinta.

Sai dai iyayenta mutanen kirki ne, ita ce dai ta mayar da kanta haka. Tamkar karin maganar nan da ke cewa  albasa ba ta yi halin ruwa ba

Ramlat ta samo irin wannan dabi’a ce lokacin da ta yi karatu a wata sakandaren ’yan mata ta kwana, inda ta hadu da wadansu kawaye da suka fito daga gidajen masu kudi.  Irin zaman da Ramlat ta yi da wadancan kawaye ne suka canja mata ra’ayi, inda take ganin ta fi karfin kowa, muddin namiji ba ya da kudi, to ba ta da lokacinsa. Ta dauki girman kai ta dora wa kanta, inda duk saurayin da ta ga ba ya da kasaitacciyar mota, to da wuya ta saurare shi.

Ramlat ta ci gaba da kasancewa a irin wannan hali har  tsawon lokaci. Sai dai abin da ba ta fahimta ba shi ne, ta shafe shekara da shekaru ba ta yi aure ba, inda shekaru suka fara yi mata nisa. Duk kyale-kyalen da take takama da su, sun fara gushewa.

Duk kawayen da take gani ba su kai ta waye ba, kuma ba su dauki rayuwar duniya a bakin komai ba, sun yi aure.  Wadansu ma sun haihu, suna zaune lafiya a gidajen mazansu.  Ita kuwa kullum sai caba kwalliya da kwambo ana ziyartar gidajen kawaye masu hali.

Sannu a hankali kawayen nata da take kai wa ziyara iyayensu suka fita da su kasashen waje don su ci gaba da karatu. Ita kuwa iyayenta talakawa ne, ba su da halin da za ta iya ci gaba da karatu a gida ma balle su tsallaka da ita kasashen ketare.

Ba a dade ba, mahaifin Ramlat ya kwanta rashin lafiya, daga baya ya rasu. Aka bar ta a karkashin kular mahaifiyarta, alhali gidan da suke zaune a ciki ma na haya ne.

An kai lokacin da kyar suke iya biyan kudin haya. An yi sa’a ma mai gidan yana da mutunci, ya fuskanci halin kuncin da suke ciki ne inda hakan ya sa ya daga musu kafa.

Rayuwa ta fara yi mata nisa, har ta doshi shekara 30 ba wani aiki take yi ba, kuma ba ta yi aure ba, sannan mahaifiyarta girma ya fara kamata. Tun bayan rasuwar mahaifinta, mahaifiyarta ta shiga wani hali na gwagwarmayar kula da Ramlat. Hakan ya sa ta yanke shawarar ba za ta sake yin wani aure ba har sai ta aurar da ’yarta Ramlat.

Za mu ci gaba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.