Yadda Na Shafe Awa 48 A Hannu Masu Garkuwa Da Mutane

0 543

A makon jiya ne Hukumar ’Yan Sandan Jihar Filato ta fitar da sanarwar cewa wadansu ’yan bindiga sun kashe wani soja mai suna Abdullahi S. a bakin aikinsa lokacin da ya yi artabu da wadansu ’yan bindiga a Unguwar Kwanar Soja a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.

Kakakin hukumar, DSP Tyopeb Terna ya ce ’yan bindigar sun kashe sojan ne kuma suka yi garkuwa da wata yarinya mai suna Hafsat Idris.

A yanzu dai yarinyar ’yar shekara 16 mai suna Hafsat Idris Gambo ta kubuta bayan ta shafe sama da awa 48 a hannun ’yan bindigar, kuma Aminiya ta tattauna da ita kan yadda al’amarin ya faru. kamar haka:

Yaya aka yi game da batun sace ki?

Ina cikin gida ranar Talatar makon jiya da misalin karfe 7:22 na dare, sai muka ji harbi a bakin  kofar  gidanmu, sai kanena ya tashi zai sauko daga sama da yake gidanmu bene ne, sai mahaifiyarmu ta hana shi fita. Ya ce ya ji harbi sai ta ce masa kada ya fita. Sai ga wani dogo, farin matashi ya shigo cikin gidan namu, amma bai rufe fuskarsa ba, yana dauke da bindiga guda biyu, daya doguwa daya karama, lokacin da ya shigo gidan sai ya fara cewa ku kwanta, ku kwanta, ina kudi da sauransu, wanda kuma ba mu bayar ba.

Daga nan wadansu matasa biyu suka shigo gidan, daya da sanda a hannunsa, daya kuma ba ya dauke da komai, da suka tambaye ni ko ni ce Hajiya (wato mahaifiyarmu ke nan), na ce musu a’a, suka sake tambaya ko ni kanwar Hajiya ce, na sake ce musu a’a. Suka ce ko ni ce ’yar Hajiya, sai na ce musu eh. Daga nan suka haura sama, inda suka faffasa mana silin din dakinmu ko za su samu kudi, amma ba su ga komai ba, haka suka fasa mana dirowowinmu, nan ma ba su samu kudi ba.

Bayan sun sauko sai suka wuce dakin mahaifinmu, inda suka samu mahaifiyarmu a ciki, a nan dai suka kwace kudadenta da ta tara a cikin jaka, daga nan sai suka tafi da mu mu uku, wato ni da yayata da kuma kanena, inda suka bar mahaifina da mahaifiyata, sai dai tun ba mu yi nisa ba, yayata da kanena suka gudu, ni kuma bayan sun kai ni bakin titi sai na ga wadansu maza gudu uku, sai na gudu zuwa wajensu, ashe duk tafiyarsu daya sai suka rike ni.

To, a tsallakenmu akwai wata makaranta da ake kira FGC, wato Kwalejin Gwamnatin Tarayya, a bayan makarantar akwai babban fili da ya kunshi gonaki da ciyayi har zuwa saman wani tsauni, sai suka fara tura ni, muka fara shiga masara haka muka ci gaba da tafiya har muka fara hawa kan tsaunin da ke bayan FGC.

Bayan mun hau saman tsaunin ne dare  ya yi muka kwana a  nan,  amma wadansu daga cikinsu sun je suka nemo abinci, inda suka je wata gona suka tono dankalin Hausa, suka zo da shi, suka ci, ni dai ban ci ba.

Da misalin karfe 4:30 na asuba sai suka tashe ni, muka ci gaba da tafiya, daga nan muka gangara kasan tsaunin, sannan suka kai ni cikin wani kogo, inda muka kwanta gari ya karasa wayewa, wato zuwa ranar Laraba ke nan, wato a ranar ba a aiki domin ana zaben kananan hukumomi a Jihar Filato, don haka babu hada-hada. To, a ranar sai suka yi magana da mahaifiyata, cewa ta ba su kudi, inda suka nemi a ba su Naira miliyan 10 kudin fansa.

 

Mutane nawa ne suka yi garkuwa da ke?

Su bakwai ne, amma hudu daga cikinsu suna dauke da bindiga, kuma suna dauke da jakar harsasai.

 

Ganin bindigogin ne ya hana ki yi musu turjiya ke nan?

Eh gaskiya, domin na tsorata, abin da yaba ni mamaki shi ne, yadda suke ba ni jakar harsashinsu in rika yin matashin kai da ita.

 

Daga nan sai me ya faru?

Sun ce in kwantar da hankalina ba kashe ni za su yi ba, ba dukana za su yi ba, su dai idan mahaifiyata ta ba su kudi za su sake ni in tafi. A ranar ina jin yadda suke shirye-shiryen zuwa fashi da makami, sun fita, amma kamar abin bai yi musu kyau ba, sai suka dawo. A lokacin da suka tafi sai suka bar ni da mutum daya, inda suka dawo da misalin karfe 9 na ranar Larabar makon jiya.

Bayan sun dawo daga fashin sai suka ce in tashi su kai ni gida, na fara murna, domin a tunanina gidan za su kai ni, sai muka ci gaba tafiya a cikin daji, inda muka rika shiga cikin kaya. Ni dai ina ta taka kaya, har muka zo bakin titi, to na san wurin, a nan na gane gaban wani gari ne da ake kira Mista Ali kusa da daffon mai da ke hanyar  Zariya da Saminaka, muka tsallaka titi muka ci gaba da tafiya, mun yi tafiya tun daga karfe 10 na safe har sai zuwa karfe 4 na yamma, a nan muka kai wata mahada ta hanyar zuwa Bauchi da na sani, ana kiran wurin Maini, sai na ce kun ce idan mun ga titi za ku kai ni gida.

Sai suka ce suna bin umarnin ogansu ne, in bi shi a baya, sai muka ci gaba da tafiya a cikin daji, inda ba mu tsaya ba sai kusan karfe 5 na yamma. Muka nemi wani wurin muka kwanta a cikin ciyayi, domin kowa ya gaji muka yi barci, har gari ya sake wayewa ranar Alhamis ke nan, suka tashe ni sannan muka ci gaba da haurawa saman wani tsauni.

 

Yaya batun cin abinci fa?

Suna ba ni abinci amma za ka daga gonaki suke cirowa, wato idan sun ballo masara, sai su dafa ko su gasa, wani lokaci su dafa dankalin Hausa, na ce musu ba na ci. To da yake lokacin da suka zo gidanmu sun shiga shagon wata mata a unguwarmu sai suka debi madara da Maltina da biskit da sauransu, to abin da suke ba ni nake sha ko in ci ke nan.

 

Daga nan fa sai yaya?

Sai muka haura kan dutse, inda suka fara magana da mahaifiyarmu ta ce musu za ta yi kokarin duk kudin da ta samu za ta kai musu, amma a ranar sun fara ba ni tsoro inda suke cewa za su tafi da ni Zamfara, za su kashe da sauransu dai. Kuma a ranar Alhamis din da misali karfe 5 na yamma suka ce in tashi mahaifiyata za ta kawo musu kudi.

Daga nan muka fara fita daga cikin dajin, muka dawo kan titi, mun dawo kan titin misalin karfe shida da wasu mintoci, a lokacin mahaifiyarmu ta karaso, ta zo da kanta ta sauka a mota, ta shigo dajin, sannan ta ba su kudi, suka ba ni wayoyin da suka diba a gidanmu, suka ce in bi mahaifiyata. Daga nan muka shiga mota, muka dawo gida.

 

Kamar adadin nawa suka karba ke nan?

A gaskiya ban sani ba, domin a baya sun bukaci a ba su Naira miliyan 10, amma suka dawo har zuwa Naira miliyan biyu, an dai hada abin da aka ba su, a gaskiya har yau ban san ko nawa ba ne. Na san dai lokacin da suka shiga gidanmu sun samu kamar Naira dubu 120, amma daga nan ban san nawa aka kara musu ba.

 

A lokacin da suka kai ki kogon dutse da kuma daji a yankin Maini, ko an hada ki da wadansu mutanen da aka yi garkuwa da su?

A’a, ni kadai ce. Mutanen da suka yi garkuwa da ni su bakwai ne, kuma dukansu Fulani ne.

 

Wane kira kike da shi ga masu aikata wannan mummunan aiki na garkuwa da mutane?

Kira gare su shi ne, gaskiya abin da suke yi ba sana’a ba ce, saboda ko addu’o’i da tsinuwa da ake yi musu za su zame musu babbar damuwa. Sannan ina rokon gwamnati ta taimake mu wajen kara jami’an tsaro a kasar nan, domin sun yi karanci, ko a nan Kwanar Soja, sojoji biyu muke da su, wanda a ranar ma an kashe daya, saura daya yanzu.

 

Na gode Allah kan kubutar Hafsat -Mahaifiyarta

Hajiya Fatima Idris, mahaifiyar Hafsat ta bayyana wa wakilinmu cewa tana godiya ga Allah da Ya rufa mata asiri Ya ba ta arzikin jama’a, inda suka yi iyakacin kokarinsu don ganin ’yarta ta kubuta.

“Ba zan iya cewa don abin da na bayar ne ’yata ta kubuta ba, illa Allah da Ya fi karfin kowa Ya sa ta kubuta, na kuma gode masa da kuma jama’a.”

Kan batun adadin kudin da ta bayar sai ta ce, “Kudi nawa ne, amma ba don na ba su kudi suka sake ta ba, na rika rokonsu, na ce musu zan iya fansar da duk abin da na mallaka idan har an samu mai saya, to zan sayar in ba su kudin don su ba ni ’yata, amma sai ba a kai ga haka ba suka sako ta, ka ga ba zan ce ga wani abu da na ba su wanda har zan gaya wa duniya cewa na ba su ba.

“Ni dai na gode wa Allah da Ya rufa mini asiri na je na karbi ’yata ni kadai ba tare da wani jami’in tsaro ba. Ina kuma yi wa masu aikata hakan addu’ar Allah Ya sa su dain,” inji ta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.