‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da ‘Yan Agajin Izala A Hanyar Zamfara

0 199

Daga Abdurrahman Abubakar Sada

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da motar ‘yan agajin Izala (Jos) sukutum (kusan mutum ashirin), ‘yan agajin mahalarta wa’azin kasa ne, daga garin Dutse (Fadar Jihar Jigawa).

‘Yan agajin sun dawo daga wurin wa’azin kasa, wanda kungiyar Jibwis (Izala Jos) ta gabatar a garin Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, bayan kammala wa’azin da kuma rufe kamfin din ‘yan agajin a jihar, zuwa garin Isa a jihar Sokoto.

A tsakanin Jibia ta jihar Katsina da Zurmi ta jihar Zamfara, wannan hanya ta shahara da ta’addanci da kuma garkuwa da mutane, haka zalika; akwai ire-iren wadannan hanyoyi a fadin jihar Zamfara.

Allah ka kubutar da bayinka, ka tsare masu mutuncinsu, ka dawo da su gidajensu saliman-ganiman.


Leave A Reply

Your email address will not be published.