Yan Boko Haram Sun Hallaka Jami’ar Red Cross
Red Cross
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
Bayan cikan wa’adin Da suka baiwa gwamnati, sun hallaka wannan baiwar Allah.
Tana daya daga cikin ma’aikatan kungiyar agajin Red Cross, Hauwa Liman, bayan wa’adin da suka baiwa gwamnatin tarayya ya cika a yau.
Yan ta’addan sunyi alkawarin cewa ba zasu kashe Leah Sharibu ba amma ta zama baiwa har abada.
Madogara Jaridar The Cable
Allah Ya jikan ta Da Rahama
Daga Bappah Abubakar