Yan Film din Hausa Sun kaiwa Bukola Saraki Ziyara

0 505

Daga Masana’antar KannyWood ‘Yan Film Din Hausa Sun kaiwa Shugaban Majalissar Dattawa “Bukola Saraki” Ziyara.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya yaba da gudunmuwar da masana’antar shirya fina-finai da ke arewacin Najeriya wanda ake kira Kannywood take bayarwa ga ci gaban kasar.
Sanata Saraki ya gana da wadansu ‘yan wasan da masu shirya fina-finan Hausa a gidansa da ke Abuja ranar Talata.
‘Yan wasan sun gana da shugaban majalisar ne karkashin jagorancin Ali Nuhu da Salisu Aliyu (Chali) da Tijjani Faraga da kuma Maryam Habila.
Ita ma uwargidan shugaban majalisar Mrs Tosin Saraki ta wallafa a shafinta na Instagram cewa: “Ina farin ciki taya mijina karbar tawagar wasu ‘yan wasan Kannywood a gidanmu don yin buda baki a jiya.
“Na gode muku ‘yan wasan hausa mata da gayyatar da ku ka yi min don zuwa inda ake daukar fim, ina Allah-Allah wannan rana ta zo, ko don na je na sake goge wa a yaren Hausa,” in ji Misis Saraki.
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.