‘Yan Gudun Hijira Sam Da 5,000 sun dawo Gida

0 276

‘Yan Gudun Hijira Sam Da 5,000 sun dawo Gida.
Alamu na nuna cewa al’ummar jihar Zamfara sun fara samun albarkacin matakin tsawaita tsaro da rundunar jami’an tsaron kasa suka dauka ya fatattaki barayi da yan bindiga da suka addabi jihar. Sama da yan gudun hijira 5,000 sun dawo muhallin su na jihar
.
.
Hakan ta biyo bayan dirar da sojoji suka yi wanda aka yi ma taken “operation sharan daji” ga yan fashin da suka tayar da kura tare da haifar da tarzoma a jihar
.
.
Tsohon kwamandan dakarun “operation sharan daji” Manjo janar Muhammed Muhammed ya sanar da haka yayin bikin mika mukamin shi ga sabon kwamandan dakarun wanda aka gudanar a garin Gusau ranar Laraba 8 ga watan Agusta
.
.
Yace al’ummomin gundumar Galadi, Kwaddi da Katuru dake kanana hukummomin Zurmi da Shinkafi na jihar da suka yi gudun hijira sun fara dawowa gida
.
.
Ya kara da cewa dakarun sun fafataki yan ta’adar dake yankin kuma zaman lafiya ya dawo garuruwan da hare-haren yan fashin yayi kaurin suna. Kai ga yanzu sojojin suna cigaba da bin sahun sauran yan bindigar da suka gudu
.
.
Daga karshe yace manoma sun fara koma gonakin su kuma harkan noma ta cigaba a wasu sassa na karamar hukumar Maradun
.
.
A nashi jawabin, sabon kwamandan dakarun Manjo janar Stevenson Olabanji yace zai yi iya bakin kokarin shi wajen dorawa daga inda tsohon kwamnandar ya tsaya wajen kawo karshen hare-haren yan bindigar a yankin.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.