Yauce Ranar Haihuwar Jarumin KannyWood Wato Sadiq Sani Sadiq Sai dai Kuma Ya Roki Kada Wanda Ya Taya Shi Murna

0 288

auraron fina-finan Hausa, Sadiq Sani Sadiq ya bayyana cewa yau, Asabar yake murnar zagayowar ranar haihuwarshi amma yana rokon masoya da abokan sana’arshi da kada wanda ya saka hotonshi da sunan tayashi murna .

Yace za’a iya mai addu’a amma yana rokon kada a saka hotonshi.
Sadiq ya kara da cewa shima kuma daga yau bazai sake saka hoton wani ba da sunan cewa yana tayashi murnar zagayowar ranar haihuwa.
Gadai sakon da ya rubuta kamar haka;


‘Salam.

Ina godiya kwarai da gaske Ga abokan Sana’a ta da yan’uwa na da masoya na wadan da suke following dina a Kan wan nan Shafi na Instagram Allah ya bar zumunci..Ina mai farin cikin sanar da Ku cewa gobe Idan Allah ya kaimu Zan Kara shekara guda a Kan shekaru na na haihuwa, da wan nan nake rokon don girman Allah Kada kowa ya saka hoto na a Instagram da Sunan Yana taya ni murna Kawai abin da nake bukata addu’ar ku akan Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya. Nima Kuma daga Rana me kama ta yau bana sake saka hoton kowa Akan page dina da sunan taya murnar ranar haihuwa, ina kaunar page dina saboda ina amfani da shi wajen tallata abubuwa masu muhimmanci nawa da na abokan Sana’a ta..wan nan shine amfanin Instagram a guri na… Da fatan za ayi min fahimta me kyau.

NAGODE’

Muna mai fatan Alheri

Leave A Reply

Your email address will not be published.