YayaNa Miji Na Hausa Novel Page 11-20

Hausa Novels

0 1,650
 • Suna zuwa ko sallama babu Hafsat ta fara magana sir munje tace baxata xu ba kuma wata kawarta ta ci mana mutunci, sir ina ganin basu da hankali ne, kallan su yayi duk yadda akai akwai abin da Ya hada ku bai kamata kuna kula su yanzu kansu Na rawa dole ku dinga musu uzuri yanzu suka fara makarantar kansu bai fara daukar zafi ba,.haka yai dan musu nasiha ta inda take shiga tanan take fita,,.sallama suka maii, shi kuma Ya karbi  assignment din nasu,. Sannan yace tura aka kira masa itta,.
  Da sallamq ta shigo, ko kallanta bai ba balle Ya amsa sallamar, tsayaws tayi tana jiran abin da zaice, ya kaii wajen 20min yana dube dube har ta gaji da tsayuwa,.
  Ajjiye takardar yayi Ya dago Ya kalleta, tare da nuna mata site, zama tayi taiii kasa da kaiiii,kallanta yake yana Nazari, ganin kallon yayi yawa yasa taja saki,kasa ksa tace malam inada aure faaaa, tsaki yayi tare da fadin nima ina dashi aiii,.
  Wato kece yar iska ko, zaro ido tayi, ina magana kikai mun rashin kunya ban kula kiba amma ki sake tabka wani kuskeren kooo? To ina san in fada miki karki bari musa kafar wando daya dake bani da kirki amma in kabi dukata zamu zauna lafiya, yanzu zan miki uzuri ne kawai danke new ce butt ki kiyaye gaba hope kin gane,? Eh na gane,mikewa tayi xata fita yace ta kuma, ke wai a wanne gari kike? Anan,amma a gidanku ba tarbiya ko kuma kin taba yin ciwon hauka ko? Zaro ido tayi ciwon hauka itta din, answer me,ej na taba, good no wonder ana ganinki anga hakan gobe ki zuu min da result naki na kin warke dan ban yadda kin gama warkewa ba, ranta in yayi million Ya baci, tsaki taja tare da fucewa fuuuuu, shima tsakin yajaaa tare da fadin zaki sani,.
  Su hanifa ne suka tare ta suna tambayarta Ya suka yi, ba komai tace musu ta dauki key Na motar ta nufi gida raii bace, dakinta taii wulli da jakar, wai tataba yin ciwon hauka, hawaye ta Fara,.
  Bayan tayi wanka ta shirya ta nufi part din mom, suna parlour gaida tayi sannan ta nufi kitchen, minal ta bita dan tayata aiki,.
  Bako kofar yayi ko sallama babu Ya zauna kusa da mom, son lafiya, tsaki yaja Wlh mun wata Yar iskar daliba na hadu da itta yau bata da tarbiya, tsaki mami taja ai kawai yaya ka koya mata hankali, to ni mai zam matane, kar ka damu bari in fada Ma yadda zakayi.,
  .
  Ai kaiii banda abin broz naga kaii prof ne amma har ka rasa abin yi, Ai kawai test zaka zuba maii uban wuya sai ka bari kuwa Ya zu hall kasan yadda zakaii ka kure ta a hall din ko kuma ranar da kaga nata zo Ba kayi test wanda baya nan ka bashi Cary-over, murnishi yai Lallai inda ke  lecturer ce za, ai muguwa, dariya tasa hmmmm ai Wlh yaya kawai daiiii Allah Ya rufa asiri amma nima faa ina sai a hankali,uhmm ni bari in wuce,kenan brozz baka dauki shawarar ba kenan? No zan gwada amma ba yanzu ba saii kaiii Ya dauki zaki,mom ni zan wuce, OK yau dad dinka zai dawo faaa,allah Ya dawo dashi lafiya, minal ce ta fito da sauri, Mom aunty ta yanke daa wuka Allah gun sai zubar da jini yake, tabe baki taii Allah Ya kare To mutunne baxaiyi aiki a hankali ba, Allah mom ba haka bane taba sani bane, to ni yanzu me kike san in mata kace tasa abu ta daure gun mana, aii tuni kwalla ta taru a idon ta haba mom, ashrim ne Ya karba muje ki dauko first aid box a daki ki gyara mata, da sauri tabi bayan shi, yaya kaga yadda ta yanke sosai ni Wlh baxan iya treating din gurin ba,kallanta yayi yadda take ta hawaye, murmushi kawai yayi in kin je kice taxu in mata treat din gurin, da sauri ta koma,.
  Aubty Yaya yace kizu yaii miki treat din gurin, noo minal bafa wani ciwo bane sosai ki barshi kawai, haba Aunty kingafa yadda kike zubar da jini, eh na gani minal zai daina, mami ce ta shigo ganin jinin na xuba yasa ta danji ba dadi, gashi kuma sarah taki zuwa, sister je ki karbo in mata treating din;da sauri ta fito a hanya suka hadu ga box din a hannun shi sai waya yake, broz kawo kaifa muke jira, kashe wayar yayi mije plz duk kin bi kin tada hankalin ki,.
  Aunty sarah kedin taya kika yanke haka? Wlh kawai ina yanka albasa kawai na yanke da hannu na, eyya aunty ki dinga kula plz, murmushi tai kawai wai yauu Mami ce yake ce mata wani tayi a hankali, turo kofar minal tayi da box din a hannunta, ashrim yana bayanta,.
  .
  Da sauri Mami ta karba ta fara wankewaw, shi kuma Ya tsaya a bKin kofa,kallan bayanta yake kamar yasan wannan kayan to a ina Ma, ohh yarinyar data maii rashin kunya, no ba Ma zai yuyu ba ace itta ba, but in itance fa, bari inga takawa yayi zuwa inda suke kafiin Ya karasa wayar shi ta Fara ringing,dauka yayi Ya fice, yana amsa call din, part dinshi Ya koma bayan Yaa gama wayar, tsaki yaja tare da fadin bari inga part Na waccan yarinyar, direct part dinta Ya nufa,.
  Itta kuwa bayan sun gama treat din gurin suka ci gaba da aikin su,.
  Parlor Ya shiga sai kamshine Ya ke tashi ta ko ina ga lemon a center table,tabe baki yayi yai ta buden daki dakin ta Ya nufa  jakarta a kan gado sai laptop dintaaa dake charge a sucket,dauka yayi Ya kunna Allah yayi baa password, kafin Ya gama search Ya Mike Ya nufi drowar dinta, hutuna Ya gani na yan gidn su, kalla yai tayi yana murmushi kawai,.
  Laptop din har ta gama search hutan ta Ya baiyaana a screen din laptop din, yana gama kallan hutunan Ya ajjiye Ya zuu gurin laptop din Ko ta kannn hutan Ma bai biba Ya fara bin ciken shi, film Ya gani kala kala, kuma duk Sun maiii, daukar laptop din yai gabaa daya Ya tafi part dinshi da itta,.
  Aunty in zaki wuce ki kaiwa broz box dinshi, Tom kawai tace haka sukaii tayi har suka gama wajen 3:30 ,part dinta Ya wuce da box din tayi wanka, kallan dakin take kamar an shigo mata,to waye zai shigo miki daki, tabe baki tayi,sai da taii sallah sannnan ta dauki, first aid box din ta nufi part din nashi,.
  Sallama take a parlour amma shiru, tsaki taja, juyawar da zatai taga wata laptop kamar ta ta, kuma gudu biyu ne agun, anyi connecting dinsu, kallan laptop din take,.
  Da sauri ta ajjiye box din ta koma part dinta, duba gun laptop din tayi ba itta Ba labarin ta,.
  Tana fita shi kuma Ya dawo daga masallaci,.
  .
  Yana shiga yaga first aid box nashi, dauka yayi ya nufi daki dashi,.
  To tama Ya akaii Ya shigo mun part dina har xai dauka min laptop dina kuma ni inasan nayi amfani da kaya Na mtswwwww, aa to why not naje na dauko kaya na kawai zaizu ya dauki kayaan mutane, to amma kika San me xaiyi da ittta haka kawai bazai daukarr miki a bu ki bashi lokaci mana, duk a zuciya take wannan maganar, bari kawai in barshi yanzu innaje Ma saifa yace wani Abun nake nema, ammma gaskiya inbai kawo min ba kafin inyi bacci ba gaskiya da matsala, haka taii ta surutanta itta one,.
  Shikuwa bayan Ya gama abin da zaiyi Ya kashe laptop din tare da fadin anjima xai kaiii mata, .
  9:00 Ya nufi part din mom dinshi dan yiwa dad sannu da dawowa, a parlour Ya tadda suuu amma sarah bata nan .
  Dad sannu da dawowa,yauwa son Ya iyali? Murmushi yaii tare da fadin lafiya qlau  to yabaku tahuu tare Ba? Eh na barta tana abune, Ya zaai kabar ta itta kadai je ka tahu da itta sannan kuma gobe ina San zamuyi magana da kaii ,OK Dad,. Haba alhaji sai kace yarinya kace anbarta itta kadai itta bata San hanya bane kawai ka dinga takurawa yaro na, kallanta yayi Lallai luba kisa a ranki haka yayanki xasu dingawa mujinsu magana ba biyayya sannan kuma a gaban kowa,allah luba ki canxa hali halinki bamai kyau bane nasan inda yaranki akakai can da bazaa musu haka ba Amman ke kina abu kamar mara tunani, ganin xancen na manya ne yasa su minal tashi, haka yaii tai mata fada bata kara cewa komaiii ba ,.
  Shikuwa ashrim part dinshi Ya nufa Ya dauko laptop din sannan ya shiga part dinta,dakinta Ya wuce direct, ba kowa sai karan ruwa dayake jii,ajjiye laptop din yayi yana kalle kalle  ganin Ya dade bata fito ba yasa Ya rubuta mata short note,.
  “`hiii dad yana San ganinki inyace ina nake kice nayi bako bye“`
  Ajjiyewa yayi Ya fice abun shi,fitar shi da muntuna ta fito daga toilet din, ganin laptop din tayi akan gado da letter,dauka tayi ta karanta, mtswww wai hii bama sallama ba, gaskiya wannan mutumin da gyara sosai kuwa,.
  .
  Bayan ta gama shirinta ta fito ta nufi part nasu mom din, yaga fitowar ta dama so yake ga ko tagaa sakon shi,.
  Da sallam ta shiga, ina wuni Dad ina wuni mom, da Fara, a Ya amsa itta kuwa mom ko kallo bata ishe taba, sarah ina fatan komai lafiya kina samun kulawa agun mijinki ko? Eh Dad ba komai muna zaune lafiya  to Allah yai muku albarka,ameen Dad, sannan kuma ki sake hakuri kinga har yanzu baku koma gidanku anzu an ajjiye ki a gidan surukaii, karki damu daya gama xaku tare zan mishi Ma magana, laaaa dad Ba komai ni zaman dan dinma Ya fi mun, aa gara daii ace mutun yana gidan shi,shikenan zaka iya tafiya,ok saida safen ku,.
  “`washe gari“`
  Suna dining Sun gama breakfast, lokacin wajen 10:00 sarah ta tafi skull,. Abubakar wato ina ma zanceb gidan ka kaki jina ko nace ka karasa gidan ka ka tare kaki ko, Wlh Dad Na kusa nan bada dadewa ba zan gama komai sai mu tare, nidai Na baka nan da wata daya Allah inbaka karaasa ba zaka fuskanci bacin raina, insha allahu dad,.
  Ni zan wuce gun aiki, adowa lafiya ameen,.
  Lecture suke sosai kuwa yayi shiru yana fuskantar lecture din wanda lecturer kabeer ke musu close friend na ashrim ne,.sai 12:00 suka fito,.
  Har office na ashrim Kabeer yaje, wato aboki kaya dani ko? A nina isa, gashi kuwa  to ya gida dan saidai ince Ya gida saboda kaki yin aure, murmushi ashrim yayi kawaii, gida qlau ai aure kuma Na kusa yin sa insha Allah to, Allah Ya kaimy ameen,haka sukai ta firan duniya,.
  .
  Su sarah ne zaune suna hutawa before a shiga wata lecture din, hanifa ke magana,sarah wai Ya kuka yi jiya da wannan malamin? Uhmm rashin mutunci yamun sannan yaja mun kunne wai dan zan tafi ban bashi hakuri ba shine wai yace nataba yin ciwon hauka kuma bani da tarbiya, zaro ido haanifa tayi Allah ki kiyayi wannan mutumin, insha Allah bazan kara bari wani abun Ya hada mu ba waccan dinma tsautdayine, Hakeey dake zauna tana chatting sai yanzu tai magana ,Sarah kin san matsalar ki kina da girman kaii kamata yayi da kika maii laifi ki bashi hakuri saboda duk rashin mutuncin mutun kikace yi hakuri kobai hakura ba sai ladaf,amma fa ke ba haka kike ba, kuma a matsayin Na malaminki bai dace kimai haka ba, murmushi taii insha allahu zan gyara kuma zanje in bashi hakuri, amma Wlh ni bawai girman kaii bane, murmushi kawai Hakeey tayi taji sosai data dauki shawarar ta,.
  Haka suka zauna har suka shiga lecture ta gaba, sai wajen 3:00suka koma Gida,.
  Direct part dinta ta wuce ta watsa ruwa, sannan ta yi jellop Na shinkafa saboda itta take San ci yauu,. Bayan ta huta ta nufi part din mom,.
  Da gudu minal ta rungumeta Aunty waec dinmu Ya fito, woww da gani anyi dace sosai Ma kuwa,duk A1 woww Allah yai mata albarka, Xama tayi Tana gaida mom,yau da sakin fuska ta amsa, haka sukai ta dan fira daga baya ta mike ta fice,.
  Mom ce da ashrim a daki, son magana zamuyi, OK mom inajinki, son nifa inasan ganin jikokina, murnushi yaii to yanzu mom me kike San ayi,? Aure nake San kayi son, aure Mom shikenan kar ki damu, kafin in gama gidana zan yi aure na baki dama ki nemomin wacca zan Aura, murnushin jin ddi tayi shikenan akwai yar wata kawata zan mata magana, mikewa yayi tare da fadin as you wish mom,.
  .
  Yau satin biyu da Fara zuwa skull kaii Ya dauki zafi, inda ashrim ki yin rashin mutincin sa,.
  Yau laraba sauri take zata tafi lecture, ashrim ne zai musu lecture kuma inka makara Baya bari a shiga,. Lokacin da ta fito shi kuma har Ya kama hanya, shaf shaf taiwa su mom sallama,gudu take a mota, amma me tana zuwa bakin titi wata katuwar mota ce ta fadi a hanya, kamar taii kuma haka ta koma, wayi wajen 50 m sannan aka samu aka matsar da motar,.
  Shikuwa ashrin ganin bata zuwa yace test kuma da exam zai hada, hankalin su hanifa Ya tashi sosai, sai leke suke wayar ta kuma a kashe,.
  Question Ya rubuta Mai sauki sosai, suna cikin yi ta karaso bakin hall din tsayawa tayi, shikuwa ko kallanta bai yibama, haka tai tsaye har aka gama test din akai submitting, ganin haka hankalinta Ya tashi, ta gefenta Ya wuce abinshi, da sauri su Hakeey suka zu inda take, sarah lafiyakika makara? Nan ta fada musu,.
  Kwalla duk ta cika mata ido tasan dole ta sami carry over a nashi subject din, Hakeey ce tai magana sarah kije ki bashi hakuri in kinyi saa Ya hakura ki tashi, noo Hakeey xan fanshe a exam , what waike meyake damunki kije ki gwada, da kyar ta yarda ta nufi office dinshi,.
  Sallama taii ta shiga, ko kallanta bai ba, sir dama zuwa nayi in baka hakuri akan abin namaka a baya am sorry sir, tabe baki yayi, no prob, amma yau nayi test and you lose saboda haka kinsan dole ki sami carry over a subject dina, murnushi taii no sir zan fanshe a exam, da sauri Ya dago Lallai yarinyar nan bata San question dinshi bane har take fada Witt full confidence zata fanshe a exam, murnushi yaii OK let see, thanks you sir tana fadanhaka ta fice,.
  Ranshi Ya baci wai xatafanshe a exam wato bata damu ba,.
  .
  Da sauri suka karasa gunta,ya akaii Ya amince zai miki? Murmushi taii kuma kunsan halin mutuminnan bashi da kirki kawai ku rabo dashi insha Allah zan samu a exam,dukkka suka ce ameen,.
  Wasa wasa, har sunyi wata da Fara skull amma bata taaaba haduwa da ashrim a gidaba sabani kuwa sunsha yinshi,.
  Yau suna parlour a zaune, duk dinsu amma sarah na part dinta tana karatu dan an kusa fara musu test,. Son dama akaaan maganaar da muka tabaaa yine, gyara Xama yayi wacce magaanaa mom, ohh ka manta kenan To auren da zakai nawa kawata magana ta amince, kuma wani satin zasu kuwo mana ziyara dan ka gansu, yariyar a skull dinku take ta kusa kammalawa, tunda ta fara maganaaa yaji wani iri amma ba yadda zaiyi dole Ya amince da wannan zabin da mahaifiyar shi ta maii, kuma ga wani tashin hankali, mahaifibshi zai amince kuwa,.
  Son baka ce komai ba,mom as you wish ba matsala Allah Ya kawo su amma mom kina ganin Dad zai amince kuwa, tsaki taja dole Ya aamince kaabaaar komai a hannuna, OK mom, minal kam haushine Ya tarar mata, cikin bacin rai tabar part din ta nufi part din sarah  ittama maaami bace komai ba amma, yaza ai ace wai yarinyat itta zata kuwa mana ziyara kamar ba mace ba,.
  Bako sallmaa ta shiga part din itta kuma tana parlour ta dage karatu take,sai ganin minal tayi rai a bace, murmushi tai waya batawa twin din mom raine, hawaye ta Fara hakan yasa sarah gyara zama subhanallah meke faruwa, da kyar ta samu ta dai hawaye sannan ta Fara magana, Aunty ba mom bace wai ta nemowa broz mataba wai Ya kara aure, abin yaba sarah dariya amma ta danne akan wannan zata dinga wani hawaye, so minal maye abin kuka a cikin nan banda abinki,ya halatta yayanki Ya auri mata har hudu To Maye aiba akaina aka Fara ba, da sauri ta karasa gun sarah, Aunty kodai ke tadaban ce ko wacce Mace nada kishi amma ke ban gani a idon kiba, Aunty kina lafiya kuwa?
  .
  Sosai tai  dariya mai isarta sannan daga baya ta tsagaita, minal gaskiya zan fada miki har ga Allah banji wani kishiba,saboda basan yayanki  nake ba kuma shima Ba sona yake ba, ke IN fada miki Ma har tau ba taba sanin Ya kamannin yayanki yake ba  kinga bai damu dani ba baidamu da yazu yaga lafiyata ba To danme ni kuma zan damu ki kwantar da hankalin ki minal Allah yasa hakan ne yafi alkhairi,.
  Aunty ina caanka dai dai yau wata daya da sati biyu da auren ko amma kice mun vaki taba ganin broz how comes, zaunar da itta sarah tayi minal wannan amana Na baki dalilin da yasa Na fada mikima kawai dan naga kin damu dani kina sona shiyasq naga mun Xama daya so plz this should be scaret, shikenan Aunty amma Wlh karki yadda broz Ya kara aure Allah karki yadda, to kawai tace mata taci gaba da abin da take,.
  Bayan Dad Ya dawone mom ke sanar masa,kallan rashin hankali yai mata, wai luba meke damunki? Tsakina da Allah inke akaiwa haka zakiji dadi ,auren yarannan yaushe akai amma kice wai aure zaiyi da wanne ido zan kalli iyayenta, haba alhaji kafasan yarannan biyyaya yai muku ya auri xabinku amma yanzu tunda yace ga wadda yake so amai uzuri mana, tsaki yaja Wlh IN kinga na amince saida dalili ways Ya dauka Ya kira ashrim din,. Ba,afi minti biyarba Ya shigo, gaida Dad dinshi yayi, Abubakar aure zaka kara ko to Allah in kaga anyi aurennan To da amincewar Sarah ne muddin taki to Wlh bazakayi aurennan ba ina fatan ka fahimta, ranshi Ya baci ya zaai xaiyi aure ace saida amincewar wata banza wannan aiba abune mai kyauba, jiyai ranshi Ya kara baci,.
  Dad ne ya kwalawa Mami kira da sauri ta fito, jeki kikira mun aunty ku ,Tom Dad, daki ta sameta tayi shirin vacci dan wajen 9:00 lokacin  Aunty Dad yana kiranki, jitaii gabanta Ya fadi, hijab tasa ta dauki wayarta suka nufu part din jjitai gabanta Na faduwa sosai, da sallama suka shiga,.
  Gaida Dad tayi ta zauna dan nesa da ashrim, Dad ne Ya fara magana sarah mijinki nasan kara aure, ya fada miki koya kuma kin amince,.
  Murnushi taii eh dad Ya fada mun zai kara aure kuma na amince, da sauri Ya juyo yana kallanta, dai dai lokacin itta Ma da gooo,.
  .
  Zaro idoo sukai a tare ba wanda Ya kara cewa kala hankan yasa Dad yake kallansu da mamaki, suna kallan juna kamar basusan junaba, dad ne yai magana lafiya akwai abin da kuke boye mun ko? Da sauri suka juya gun Dad gaba dayansu sun shiga damuwa, sarah karki boye mun wani abu ki fada mun gaskiya, shiru tayi itta hankalinta Ma baya gunshi she is shocked,kallanta dad yake yaso Ya fahimci wani abu, amma kuma daii yai shiru, sarah kina jina kuwa? Da sauri ta dago eh dad, sarah karki cuci kanki in kinsan baki San aurennan Wlh baza ai ba dududu wata naya da yin auren ku? Allah ba komai Dad, shikenan Allah yai miki albarka,.
  Kai kuma Ya mukayi da kaii zancen komawa gidan ka? Eh Dad na kammala komai ina ganin kawai a bari sai su tare in anyi auren, kallan banza Ya watsa maii sai anyi aure aikuwa kayi kadaaan, kallan sarah yayi, kin amince sai anyi ko kuma zaki kuma before a ayi auren? Aa Dad zan koma before auren, kallanta ashrim yayi ya galla mata harara danfa shi bai wani kammalaba, tsaki mom taja nidai ban taba ganin abu irin wannnan ba ace wai abu sai antabiyeta kuma baza, a tambayi mai abun mtswww,. Tsaki Dad yaja zaku iya tafiya, da sauri sarah ta Mike ta nufi part dinta sai sauri take abunta,yana biye da itta a baya tsaki yaja jibi yadda take sauri kamar wata Mota mstww,,.
  A parlour ta zauna taya Ma xaai haka ta faru wai sir ne mijin ta kuma malaminta kuna yayanta, OK dama yasan ni matar shice shiyasa yake mun rashin mutunci dan baya sona, tsaki taja mina din ba sanshi nake ba aiiii,.
  Yana shiga part dinshi yayi wanka sannan yai shirin bacci, dan shi har yanzu bai yadda ittace matar shiba kawai gani yake gizo take maii, tayama xaai ace ittace matarshi yarinyar da farkon haduwar su rashin kunya ta fara mai yarinyat da baya so sannan kuma ace ittace matar shi kuma dadim dadawa mahaifinshi yafi fifitata akan shi sai abin da tce shi zaai, tsaki yaja tare da kara jannn barko, amma,.
  .
    Washe gari
  Yakama Sunday ne,saboda haka bata tashi da wuri sai wajen 11:00 wanka tayi tasa kayanta ta nufi part nasu mom, Mom ce kawai a parlour su minal Na kitchen, ina kwana mom? Lafiya qlau, zauna za muyi magana, ba musu ta zauna  sarah nasan son bai wani fada miki zaiyi aure ba kawai daii kin fada ne, naji dadin abin da kika yi sannan kuma ni bawai dan komaii nake sann Ya kara aure ba saidan gaskiya bana San ace son dina da daya zai haifa,cikin rashin fahimta ta kalle ta eh kinsan ku jinin ku da daya kuke hai, uwarki ma itta kadai aka haifa sannan gaki kema ke daya ce saboda ni gaskiya bana san dana Ya haifi da daya,murmushin akaici  tayi, ko shin wannn matar ta manta da dayanma wasu basu samu ba oho mata, Allah Ya shirya, kuma insha allahu ni bama zan zauna da danta ba, Mom ce ta dawo da itta daga tunaninta, ina fatan wannan bazai sa kiji haushi ba? Ba komai mom Allah yai mana jagora ,ameen
  Sannan kuma ran laraba amarya za ta kawo min ziyara saboda ki shirya tarba dan ke zakiyi aikin komai inma kina da lecture ranar saidai ki hakura, ina fatan kin gane,? Eh mom, OK zaki iya tafiya,.tana mikewa wayarta ta Fara ringing,.
  My mom ta gani, waje ta fita sannan ta dauka, hello Mom, ina kwana? Lafiya qlau sarah shine ku dan nemanmu baki yi ko wato kinyi aure ko, laaa mom Wlh ba haka bane, to ya gida ya mijin naki? Lafiya qlau, sarah sai kina hakuri fa nasan ba wani jin dadin zaman wannan gidan kike ba, ba komai mom aure Ma zaiyi, eh dad dinshi Ya fada mana, da yaki fada wai yana ganin bai dace ba, kedai kawai kici gaba dayin biyyay insha alllahu mom, tom sai anjima, Tom mom ki gaida baba, .
  Kace wayar tayi tana murmushi, tana juyowa ta ganshi a bayanta Ya wani harde hannaye,.
  .
  Saida gabanta Ya fadi, yasa fararen kaya, komai fari fuskar a hade kamar wani wanda bazaiyi dariya ba,.
  Ta gefen shi tazu wucewa yaii saurin sa hannu, kallanshi tayi, tabe baki yayi tare da nuna mata kujerar gurin alamartl ta zauna, ba musu ta zauna, shima zaman yayi, saida Ya dauki wajen 10m yana kallanta baice kala ba, itta kuwa banda tsaki ba abinda take yii a ranta, a hankali Ya Fara magana kamar yadda hubby take in tana waya da sauriyinta .
  Wato dama ke rashin kunyar da kike mum a makaranta dan kinsan ni mijinki ne kuma yayanki ko? Shine kike wani fasa kaii ko, ai sai yanzu Na gane, sannan kuma jiya nace sai anyi aure zan tare a sabon gidana kince ba haka ba koo, dakyau to inasan kije ki fadawa Dad kin janye sannan kuma ki dauka wannan tarewar ba wani jin dadin ta zakiyi ba ina fatan kin gane? Murnushi taii tare da fadin pardon dan Wlh duk banji me kace ba, da sauri Ya kalleta jiyake kamar Ya shako ta, tsaki Ya jaaa tare da mikewa yabar gurin, itta haka,.
  Kitchen taje gun su minal suka ci gaba da aiki,aunty sarah ki shirya zamuje super market da yaya ashrim, no kuje kawai ni baxanje ba, aikuwa Dad yace dole kije, OK shikenan,.
  Haka suka gama aiki sai wajen 12:00 suka gama, part dinta ta nufa ta sake wanka,.
  Yana garden, Dad Ya kira shi,ka kira mun sarah kuzu tare, tom kawai yace tare da mikewa Ya nufi part din mata,.
  Laptop dinta a parlour da litta fin jutting dinta na makaranta,.
  .
  Xama yayi kusa da laptop din, hutan tane akaii, tabe baki yayi tare da fadin tayi kyau, jutting book din Ya dauka yana dubawa, ku wannen subject da nashi kannin saboda book din babbane, haka yaii ta dubawa har yaje gun subject dinshi, dubawa yake komai ta rubuta, tunowa da sanda tace zata fanshe a exam yayi, wani kayattacen murmushi yaii, Ya tattara gaba daya gun jutting din Ya yage, dai dai lokacin ta fito ta tsaya tana kallan idon Allah hankalinta Ya tashi sosai, da sauri ta karaso tana kallan shi,shima kallan nata yayi,lafiya ka yaga mun littafi, ki gude Allah Ma daba duka Na yaga ba, mikewa yayi tare da fadin dad yana kiran mu, ban ta kadduna ,ai kina da karfi ko kuma in kin ciki ke mara kunyace inna ajjiye kije ki dauka, yana kaiwa nan Ya fice,.
  Tsaye taiii zuciyarta banda yafasq ba abin da take ranta Ya baci sosai, hawayene suka fara zarya a face dinta, wayarta ce ta Fara ringing, Hakeey ta gani, hello sister Ya kike, lafiya qlau sister, plz sister gobe ki zu mun da jutting book dinki na, sir ash, OK Ya naji muryarki haka,?ba komai sai mun hadu goben, OK bye,.
  .Hijab dinta ta dauko a daki ta wuce part na mom, duk kowa yana zaune, da sallama ta shiga, ina wuni Dad? Lafiya qlau daughter, garan murya yayi, dama inasan son zai kaiki sabon gidan da zaku koma yauu zaki gani zaki zabi inda yai miki duk komai iri daya ne, sannan zaku biya kasuwq ku siyi abin da kuke bukata, OK Dad ba matsala, shikenan yanzu kuje ku shirya, Tom Dad, mikewa sukai harda su minal, tare suka fito da ashrim din, kallan ta yayi yaga alamar tayi kuka, nan da nan farin ciki Ya mamayeshi Ya fara ramawa,,.part dinta ta wuce shima Ya wuce nashi.
  Takakdun Ya Fara dubawa ,dole tace zata fanshe a exam mana tunda ta dauke komai yay rainin hankali kawai,.
  Sai wajen 4:00 suka shirya, Minal ne da mami a gun mota amma babu alamar ashrim da sarah, tsaki suke ta jaaa, cikin fushi minal ta nufi part dinsu a hanya taki kuro da ashrim, haba yaya tun dazun muke ta jranku amma kunje kun zauna, kallanta yayi tare da fadin to dakeni mana, ni aiba cewa nayi zan dake ka ba, tare suka juya ,kallanta yayi tare da fadin ina wannan yarinyar take? Wacce yarinyar, harara Ya watsa mata ohhh Aunty bata fto ba  je ki kirata ko kuma in tafi, Allah na gaji yaya ohhh baxakiba ba kenan? Zanje yi hakuri,.
  .
  Daki ta shiga Aunty wai Me kike har yanzu baki shirya ba? Minal bana San tafiya kuje kawai, what aunt Dad ne fa yace kije kuma wannan fitar saboda ke Za, ai sannan kice bazakije ba haba sister, dad yana ganin hankalinki sosai Dan Allah ki tashi ki shirya mu tafi, minal yau yayanki Ya bata mun raii sosai Allah ba nasan fitar nan kawai Ban San Ya Xanyi bane,.
  Ji sukai ance To nimaa din so nake in fita dake ne, kinga malama ina da abun yi in Baki fiito ba keki sani, maganar ta batawa minal rai maimakon Ya Ba matarshi baki Amman yake fadan haka,tsaki taja tare da ficewa,dakin Ya shi Ya bude drower gun kayanta, wasu blue Ya Gani Ya fito dasu tare da mayafinsu, gashinan Na baki nan da 5m ki shirya ina parlour ina jiranki, kuma Wlh in baki shirya ba Dad zan kira ince kinki tafiya ko kuma in kira mamanki ince inamiki magana kinki ji, yana kaiwa nan Ya fice abun shi,tsaki ttaja, tare da mikewa dama tayi wanka morri ta xauna, tasa wannan tasa wancan, har wajen 7m sannan ta gama, tasa kayan,. Sannan ta dauki nayafin ta yafa  tsayawa tayi a gaban madubi ta kalli kanta,sai juyawa take, dai dai lokacin ya turo kofar,da sauri ta dauki purse dinta, tare da fadin Na gama, tabe yayi tare da fadin muje, tare Suka fito, kallanta yayi baxaki rufe kofar bane? Eh kawai tace mashi,.
  Mota suka shiga Suka nufi gidan, gidan Ya hadu ba karya part uku ne, biyu a gefe sai nashi a tsakiya,.haka suka gama zagaye zagayen su sannan suka nufi, kasuwa,.
    Fitowa sukai suna tafiya, jitai ance AISHA AMINU SARAH da sauri ta juya zaro ido tai tare da fadin Zainab Aminu Zee, Ashe zamu kara haduwa, tsaki ashrim yaja suka wuce shida su minal, Zainab a ana garin kike? Eh mana aure nake anan, Lallai kam tun rabowar secondary sai yanzu, yanzu Ma Allah ne yayi samu hadu,wlh kuwa haka sukai ta hira ta yaushe gamo, .
  Dai dai zasu shiga market din suka ci karo da Kabeer sai sauri yake, mami ce tai saurin cewa, yaya Kabeer, juyowa yaya aa twin na mom anfito yawu wlh kuwa, aboki Ya Gida Ya zaman kadaici tunda kaki kayi aure ni madam ce ta aiko ni sai sauri nake karta yi fushi, zaro ido minal tayi Yaya Kabeer, ai yaya yayi aure bai fada maba? Kallanta yayi ni kikewa wasa, Allah Yaya dagaske nake tare muke da itta Ma, kallan mami tare da fadin wai haka, daga kaii tayi alamar eh, kallan ashrim yayi, shikumq Ya juyar da kaii, cikin fushi Ya nufi motar shi,.
  Kallan minal yayi tai saurin dauke kaiii,
  “`.
  Da sauri Ya nufi motar yana kiran khabeer amma ko kllanshi baiba Ya wuce tsaki yaja tare da fadin kaji dashi,.
  Sallama sukai da Zainab ta nufi inda suke,kallan minal tayi  yana ga yayan naki Ya wani bata raiii? Tabe baki taii wai Dan fadawa abokinshi yayi aure shine yake cika yana batsewa, murmushu kawai tayi suka nufi cikin market din, gun kayan kwalliya su minal sukai itta kuma tabi wajen kayan sawa, Arabian gowns take diba masu kyau  daga nan tai wajen turararr rika anan ta hadu da ashrim Ya dauki wannan Ya ajjiye Ya dauki wannan Ya ajjiye, tabe baki taii tana duba Wanda yai mata, perfect man ta gani, turaren Ya kwanta mata sai taji tana San daukawa ashrim amma tana tsoran disgi, ajiyar heart ta sauke ta dauko turaren, yaya ashrim kaga wannan turaren da Gani xaiyi kamshi mai dadi, kallanta yayi yaune ta kira shi da ashrim  tabe baki yayi ni kuma bana so,.
  Batace komai ba tasa a kayanta tai gaba, pad ta gani Kala Kala,ta dauki wannan ta ajjiye ta dauki wannan ta ajjiye, tana haka har yazu gurin da take tsayawa yayi yana kallan idon Allah in ta dauki wannan saita yi tsaki ta ajjiye, tsaki yaja tare da karasawa gurin,tana ganin shi ta boye ta hannunta a baya, abun dariya Ya bashi amma Ya dake, dauko always yayi tare da sa mata a kayan, ina tunanin wannan zatafi ki ajjie wannan ta hnnun naki kuma kiyi sauri ki fito zamu wuce, yana kaiwa nan Yai gaba abun shi, tsaki taja tare da fadin dama da gani dan iska ne in Ba haka ba ina yasan wani wadda tafi da wadda bata fi ba mtsww, kuma bazan dauka bama, har xata mayar sai kuma tai tsaki ta ajjiye ta hada da wadda tai mata,. Agun biyan kudi suka hadu da su minal, Sun yi uban shopping kamar wanda zasuyi kayan lefe,.
  Haka suka nufi motan, aka sa musu kaya sannan suka nufi Gida,.
  • Sai wajen 6:00 suka karasa gida yana parking, kuwa ta bude ta fice amma side na sarah a luck yake, kallanshin taii taga ko a jikin shi Ma danna wayar shi yake,.

Ku Cigaba da Ziyartar wannan Shafi domin cigaban wannan Littafi dama wasu da dadan Littafan.
www.ArewaRulers.com

WhatsApp: 08161892123

Leave A Reply

Your email address will not be published.