Zamu rinka neman shawarar malaman addini – Shugaban MOPPAN

0 221

Sabon shugaban kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Najeriya (MOPPAN), reshen Jihar Filato Alhaji Ibrahm Lawal Ibrahim ya bayyana wa Aminiya cewa sun fara aika wa malaman addini a jihar wasiku domin neman shawara a wata tattaunawa da Aminiya.

Ko za ka fara da gabatar da kanka?

Sunana Ibrahim Lawal Ibrahim, sabon zababben shugaban Kungiyar Masu shirya fina-finai wato MOPPAN reshen Jihar Filato.

Yaya kake shirin kawo canji a kungiyar?

Idan ana so a tabbatar da adalci to a baiwa kowa dama ya nuna bajintarsa. Tun da can ina da da bukatar in bayar da tawa gudunmuwar a wannan masana’anta, wanda ba zai yiwu ba sai na samu damar zama shugabanta. Wannan ne ya sa na kawo kaina wajen membobi kuma suka karbeni har ta kai na samu goyon baya da kuma goyon bayan masu gidana a harkar fim na kai ga samun nasarar zama shugaba.

Wane hanyoyi za ka bi wajen ciyar da kungiyar MOPPN a Jihar Filato gaba?

Hanya ta farko da nake gani zan kawo ci gaba shi ne na yi kokari na ga an hada kai. Hanya ta biyu kuma ita ce mu fahimci juna mu mus an cewa ba mu da burin da ya fi tsira da mutuncinmu ta wannan sana’ar da muke yi. Idan fa ba mu koma karantarwar da Al‘kurani ya yi mana ba na cewa mu hada kanmu kada mu rarraba a rayuwa, ba za mu samu nasara ba. Idan aka hada kai za a cimma nasara kuma ba za a ji kunya ba.

Me ya sanya masu shirya fina-finan Hausa ba ku kiran malaman addinai suna daukar nauyin shirya fim da ke koyar da zamantakewa ba?

Muna yi. Watakila ka karanta ne ko ka ji a wata kafar yada labaran lokacin da na kaddamar da yakin neman zabena, na yanke shawarar kiran malaman addini musulunci da na kirista mu rika shirya taron karawa juna sani domin su zo su ba mu shawarwari ta yadda za mu ci gaba, mu gyra zamantakewarmu ba mu yi abu ba a koma gefe ana yin Allah wadai ba. Komai ya tashi sai a ce ‘yan fim ne, alhalin ba su zuwa su ba mu shawarwari. Magana idan ba ka gyara ba, ai ba shi da wani amfani. Dan Aadam zai iya yin kuskure idan ba a kira an gyara mana ba ka ga zan iya cewa a mana gyara. Don haka za mu rika gayyato malaman addini baki daya; na musulunci da na kirista domin kungiyar MOPPAN ba ta musulmi ba ce kawai
Ko kana da sakon ga masoya fina-finaku?

Sakona ga mabiyana da shugabannin kungiyata shi ne ina neman goyon bayansu domin samun hadin kai ‘ya’yan kungiyar, domin idan wani abu ya baci baza a ce Ibrahim Lawal ne ya lalata ba domin wanda ma ya lalata shi ma watarana zai iya zama shugaba. Amma idan muka taru muka gyara ka ga za a ce shugabannin kungiyar ce baki daya suka gyara ko kuma kungiyar MOPPAN ta gyara.

Ina kira ga membobinmu da shugabannin kungiyarmu da don Allah mu yi kokari mu hada kanmu mu ba da goyon baya tare da bayar da shawarwari da za su sanya mu ci gaba. Al’umma kuma abin da duk suka gani mun aikata a fim, ba halayyarmu ba ce, muna kokarin nuna wa al’umma halin da ake ciki ne domin su hankalta kuma mu fadakar.
©leadershipayau.com

Leave A Reply

Your email address will not be published.