Zan Nuna Wa Jaafar Jaafar Yadda A Ke Hada Bidiyo, Cewar Rashida Maisa”A

0 306

Zan Nuna Wa Jaafar Jaafar Yadda A Ke Hada Bidiyo, Cewar Rashida Maisa’a

Mai ba wa gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin siyasa, RASHIDA ADAMU ABDULLAHI MAISA’A, ta yi fice a fagen shirya finafinai da kuma farfajiyar siyasa a jihar Kano.

Me za ki ce game da bidiyon da a ka saki kwanan nan a na zargin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da amsar cin hanci?

Da ya ce akwai bidiyo, ai ni ’yar wasan kwaikwayo ce; na san yadda a ke tace hoto (editing).

Na fada cewa, zan saki bidiyo kamar yadda a ka nuna mai girma gwamna ya na mika kudi ba tare da a na ganin mutumin da ya miko kudin ba kuma tsawon shekarun da a ka yi a na amsar kudin kayan mai mika kudin guda daya ne, kamar aljanu ne su ke mike ma sa tunda ba a nuna ma na mutumin da ya kawo ba na wanda har za ka iya shiga ofishin gwamna ka dauke shi, to ta ina ya saka kyamarar?

An ciro daga LEADERSHIP A YAU

Leave A Reply

Your email address will not be published.