Zanga Zangar Ranar Ashura : Jami’an Tsaro Sun Bude Wuta Akan ‘Yan Shi’a

Shi'a

0 265

Zanga Zangar Ranar Ashura : Jami’an Tsaro Sun Bude Wuta Akan ‘Yan Shi’a.

Rahotanni daga birnin Zariyan Jihar Kaduna sun bayyana cewar rundunar ‘yan Sandan jihar sun bude wuta gami da watsa barkonon tsohuwa akan dubban ‘yan shi’a Maza da Mata wadanda ke gudanar da zanga zangar ranar ashura, domin nuna bakin ciki da alhinin su akan kisan da akayiwa jikan Annabi wato Sayyidina Hussain a Karbala.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar, tun da sanyin asubahin ranar yau ce ‘Yan Shi’an suka yi dafifi suka cika birnin na Zazzau sannan suka rurrufe hanyoyi suka hana jama ‘a gudanar da harkokin su na yau da kullum, suna rera wakokin tsinuwa da La’antar wadanda suka aiwatar da kisan Sayyidina Hussain, hakanan kuma sun cigaba da La’antar wadanda suka kira a matsayin shugabanni masu koyi da azzaluman farko, inda suka rinka kiran sunan Buhari da Buratai da El Rufai suna tsine musu, lamarin da ya haifar da hatsaniya da kuma tarzoma a birnin.

Jami’an tsaro sun yi kokarin dawo da bin doka da oda a cikin birnin sai ‘Yan Shi’an suka mayar da martani a garesu ta hanyar jifarsu da duwatsu da yi musu ihu, dalilin da ya sanya jami’an tsaro bude musu wuta da watsa tafasasshen ruwan zafi a kansu.

Saidai babu labarin rasa rai ko guda, amma duk da haka rahotanni sun tabbatar da raunata ‘Yan Shi’an da dama wadanda akasarin su kauyawa ne da suka fito daga sassa daban daban na yankin Arewacin Nijeriya domin karbar kiran jagororin su.

#Mikiya

Leave A Reply

Your email address will not be published.